Mutane sun mutu a wurin rabon kudi a Borno

Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya sun ce, a kalla mata biyar sun rasu sakamakon tirmitsitsin da aka samu a wurin rabon kayan agaji da suka hada da kudi da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ke bai wa dubban jama’a a Gamborou.

Wata majiyar asibiti ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, an kai gawarwakin mata hudu da karamar yarinya guda asibitin tare da wasu mutane bakwai da suka samu rauni.

Umar Kachalla, daya daga cikin ‘yan sa-kai ya tabbatar cewa, an samu asarar rayukan ne a tirmitsitsin a yayin rabon kudi da turmin atamfa.

A kalla ‘yan gudun hijira dubu 70 ke samun mafaka a Gamborou tun bayan da sojojin Najeriya suka karkade mayakan Boko Haram daga garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *