Muna neman tallafin corona daga tarayya- Gwamnonin Arewa

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya na neman tallafi na musamman daga gwamnatin tarayyar kasar don yaki da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 a yankinsu.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya kuma gwamnan jihar Filato, Solomon Lalong ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Darektan Yada Labaransa, Dr. Makut Macham ya fitar a ranar Litinin jim kadan da kammala taron da gwamnonin suka gudanar ta hanyar sadarwar wayar taroho.

Gwamnonin sun gudanar da taron ne don tattaunawa kan batun da ya shafi cutar coronavirus da kuma illarta ga yankin arewacin Najeriya.

Shugaban gwamnonin ya yi korafi cewa, gwamnatin tarayya ta bai wa wasu jiohin kasar tallafi na musamman don yaki da coronavirus, amma kawo yanzu babu jiha ko daya a arewa da ta samu irin wannan tallafi duk da cewa, cutar ta bulla a ynkinsu.

Daga cikin jihohin da coronavirus ta bulla sun hada da Kano da Katsina da Kaduna da Bauchi, yayin da jihohin ke cewa, ba su da isasshen kudin yaki da wannan annoba mai yaduwa tamkar wutar daji.

A kwanakin baya, shugaban Nejariya Muhammadu Buhari ya bai wa jihar Lagos tallafin Naira biliyan 10 don tunkarar cutar coronavirus.

Leave a Reply

Your email address will not be published.