Masu arzikin duniya sun tausaya wa kasashe matalauta

Gungun kasashen G20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, sun amince da matakin jinkirta wa kasashe matalauta biyan bashin da ake binsu da a kalla shekara guda saboda yadda annobar coronavirus ta yi wa tattalin arzikinsu illa. 

Baya ga wannan rangwamen, kasashen na G20 da suka gudanar da taronsu a yammacin ranar Laraba, sun kudiri aniyar bai wa kasashen tallafin kayakin yaki da annobar ta COVID-19.

Galibin matalautan kasashen a cewar G20, na fama da nauyin da ke kansu na yaki da annobar, sannan kuma ga matsalar tattalin arziki wadda tsananta sakamakon daukar matakain takaita zirga-zirgar jama’a don dakile yaduwar coronavirus.

Ministan Kudin Saudiya, Mohammed Al-Jadaan wanda ke shugabancin gungun G20, ya ce, za su samar da tallafin Dala biliyan 20 wanda za a yi amfani da shi wajen sayen kayayyakin yaki da cutar ta COVID-19 don rarraba wa kasashen 76 galibinsu a nahiyar Afrika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *