Coronavirus ta sake kashe wasu mutane hudu a Saudiyya

Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa, annobar coronavirus ta sake kashe mutane hudu, sun mutu a kasar a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. A yanzu jumullar wadanda suka mutu a kasar ya kai 84. Mai magana da yawun ma’aikatar, ya bayyana cewa mutane hudun da suka mutu ba ‘yan Saudiyya ba ne, kuma suna fama da wasu cutukan na daban, Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito. 

An kuma tattaro cewa shekarun mamatan ya kama daga 35 zuwa 89. 

Har ila yau, kakakin ma’aikatar ya ce an samu sabbin mutane 518 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, wanda jumullar adadinsu ya kai 6,380. “Daga cikinsu, 990 sun warke bayan samun rahoton 59 da suka warke a cikin sa’a 24 da suka wuce,” a cewar ma’aikatar lafiyar. 

A wani labarin kuma, mun ji cewa ma’aikatar lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya ta bayyana cewa mutane su shirya gudanar da Sallar Tarawihi a gidajensu saboda ba za’a bude Masallatai ba. Sallar Tarawihi wacce aka fi sani da Sallar Asham, wasu raka’o’i ne da ake gudanarwa bayan Sallan Isha’i a cikin watar Ramadana. Gwamnatin Saudiyya ta ce sam ba zata daga dokar rufe Masallatai ba sai cutar Coronavirus ta kare gaba daya. Jaridar Al-Riyadh ta ruwaito Ministan lamuran addinin Musulunci, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, da cewa Sallolin farilla biyar da aka dakatar sun fi Tarawihi muhimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *