Coronavirus ta kara wujijjiga kasuwannin hannayen jari

Kasuwannin hannayen jari na duniya na ci gaba da durkushewa, inda suka sake tafka gagarumar asara a ranar Laraba sakamakon tasirin annobar COVID-19, yayin da farashin gangar danyen mai ya sake faduwa duk da matakin da aka dauka na rage fitar da gangunan mai da kusan miliyan 10 a kowacce rana.

Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IEA ta ce, mai yiwuwa shekarar 2020 da muke ciki, ta zama mafi muni a tarihin bangaren bunkasar fannin makamashi na duniya.

Hukumar ta IEA ta ce, bukatar danyen mai a duniya zai ragu da a kalla ganga miliyan 29 kowacce rana a cikin wannan wata na Afrilu, sama da abin da kasashe masu arzikin man fetur a duniya suka kayyade.

Faduwar farashin gangar danyen man zuwa kasa da Dala 24, ya yi tasiri kan kasuwannin hannayen jari na duniya da suka kunshi kamfanonin mai, bayan da kasuwannin a Turai suka tafka asarar sama da kashi 3 cikin dari a jumlace.

A Talatar da ta gabata, Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya da a kalla kashi 3 cikin 100 a shekarar 2020 da muke ciki, yayin da tattalin arzikin Amurka mafi karfi a duniya, zai durkushe da kusan kashi 6.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *