A Najeriya, Cibiyar Yaki da Cutuka a kasar ta ce, an samu mutane 51 da aka tabbatar cewa sun kamu cutar coronavirus a kasar a ranar Juma’a, adadi mafi yawa da aka samu a rana guda tun bayan bullar wannan annoba da ta kama mutane 493 a fadin kasar.
Sabbin alkaluman na nuni da cewa an samu mutanen ne a jihohi 8, da suka hada da Lagos-32, Kano– 6, Kwara– 5, Abuja, Katsina da Oyo kowanne na da mutane 2, sai kuma mutum guda-guda a jihohin Ogun da Ekiti.
Cibiyar ta NCDC ta ce an samu karin mutane 4 da suka rasa rayukansu, abin da ya sa adadinsu ya tashi zuwa 17 a maimakon 13.