Afrika na bukatar karin Dala biliyan 44 don yaki da corona

Babban Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, sun bayyana cewa, Afrika na bukatar karin Dala biliyan 44 don yaki da cutar coronavirus a nahiyar.

Wannan na zuwa ne bayan manyan kasashen duniya sun jinkirta wa Afrikar biyan tarin basukan da ke wuyanta da a kalla shekara guda domin ba ta damar tunkarar annobar coronavirus.

Bankin na Duniya da Asusun IMF da suran cibiyoyin tallafin kudi, sun samar da Dala bilyan 57 don agaza wa bangaren kiwon lafiya da tattalin arzikin Afrika.

Kazalika an samu wasu cibiyoyi masu zaman kasu da suka bada Dala biliyan 13 a matsayin tallafi ga Afrika,

Sai dai duk haka, Bankin Duniyar da Asusun IMF, sun ce har yanzu akwai gibin Dala bilyan 44, domin kuwa a takaice, Afrika na bukatar Dala biliayn 114 don samun damar yaki da cutar coronavirus a cikin wannan shekara ta 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *