An gudanar da jana’izar Abba Kyari a Abuja

An gudanar da jana’izar Mallam Abba Kyari, shubagan ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya rasu bayan fama da jinyar cutar coronavirus.

A safiyar wannan Asabar ce gawar marigayin ta iso birnin Abuja daga jihar Lagos, kamar yadda Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya sanar, inda tuni aka binne shi a makabartar Gudu.

Mutane kalilan ne suka halarci sallar jana’izar bayan fadar shugaban kasa ta ce, za a gudanar da jana’izar cikin sirri.

Tuni fitattun ‘yan siyasa a Najeriya suka fara aike wa da sakon ta’aziya ga shugaba Buhari da suka hada da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Kakakin Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da gwamnan Kogi, Yahya Bello da takwaransa na Delta, Ifeanyi Okowa, sai kuma Jam’iyyar adawa ta PDP.

Kyari dai ya kasance mutun na farko daga jerin manyan ‘yan siyasar Najeriya da cutar coronavirus ta kashe a kasar.

A ranar Juma’a Kyari ya yi ban-kwana da duniya a wani asibiti mai zaman kansa da ke jihar Lagos, makwanni hudu da aka tabbatar cewa, ya kamu da cutar coronavirus bayan dawowarsa daga kasar Jamus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *