Za a rufe Masallacin Kudus a watan Ramadan

Majalisar da ke kula da Masallacin Birnin Kudus ko kuma Al-Aqsa, wanda shi ne na uku mafi daraja ga Musulmin duniya, ta ce za ta rufe Masallacin ga al’ummar Musulmi a lokacin azumin watan Ramadan mai zuwa saboda annobar coronavirus da ke ci gaba da lakume rayuka.

Majalisar wadda ke karkahsin gwamnatin Jordan ta ce, daukar matakin ya biyo bayan shawarar da Majalisar Malamai da masana kiwon lafiya suka bayar.

Kodayake majalisar ta bayyana daukar wannan mataki a matsayin abin takaici, tana mai umartar Musulmai da su gudanar da sallolinsu da addu’o’insu a gida a cikin watan na Ramadan don kare lafiyarsu.

Sai dai za a ci gaba da kiran salla sau biyar a rana a Masallacin, sannan kuma za a bai wa ma’aikatan Masallacin damar shiga cikinsa.

Ana sa ran fara azumin Ramadan na bana a ranar 23 ga watan Afrilu da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *