Duk da dokar tilasta zaman gida, baƙi 2,500 sun fice daga Najeriya

Masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa, ci gaba da shige-da-ficen jiragen sama a birnin Legas da kuma Abuja ka iya kara adadin mutanen da za su harbu da cutar corona. Ana rade-radin cewa jiragen da ke jigilar baƙi daga Najeriya zuwa kasashensu na kuma sake shigo da wasu fasinjojin daga kasashen da annobar cutar coronavirus ta yiwa lullubi. 

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wannan jita-jita. Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, akwai akalla baƙi 2,500 da aka fice da su daga Najeriya daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da kuma Murtala Muhammad da ke birnin Ikko. 

A rahoton da jaridar ta wallafa, ta ce cikin makonni biyu gwamnatin wasu kasashe sun yashe al’ummominsu daga Najeriya da suka hadar da Amurka, Canada, Birtaniya, da kuma Faransa. Da ya ke bayyana ra’ayinsa, wani ma’aikacin lafiya, Michael Ajagun, ya bayyana takaicin sa a kan lamarin. 

Ya ce “ina jin takaicin yadda a baya-bayan nan na lura da yadda jiragen saman kasashen ketare ke shigowa Legas.” “Ba daidai bane gwamnati ta shinfida dokar tilastawa mutane zaman gida kuma ta rika lale maraba da shigowar baƙi ‘yan kasashen waje, wadanda wasunsu ke fitowa daga wuraren da annobar cutar coronavirus ta yi kamari.” “Cutar coronavirus bakuwar cuta ce da ta samo asali a wajen Najeriya, saboda haka babu ma’ana yayin da gwamnati ta bari jiragen waje suka ci gaba da shige-da-fice kuma a sa ran dakile yaduwar cutar a nan kusa.” Ya zuwa yanzu dai akwai mutane 442 wanda cutar coronavirus ta harba tun bayan bullarta a kasar kamar yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *