Ana gobara a Hedkwatar INEC dake Abuja

Labarin da muke samu da duminsa na nuna cewa hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja na ci bal-bal yanzu haka. The Nation ta ruwaito cewa gobarar ta fara ne lokacin Azahar kuma har yanzu tana zalzala. Wannan shine karo na uku da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa babu maaikata a ofishohin. An umurci maaikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja. 

A ranar Larabar nan, 14 ga watan Afrilu 2020, gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja. Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki. 

Hakazalika a makon jiya gobara ta lashe ofishin akawunta janar na tarayya wacce akafi sani da baitul malin gwamnati dake Abuja. Bayan gobarar ta kwashe lokaci tana ci bal-bal karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar. Yace “Mun duba sashen adana bayanai mun ga gobarar ba ta shafi bangaren ba, duk da ta taba dakin wasu na’urori da ke sanyaya wurin adana bayananmu. Ba mu kammala bincike da sanin barnar da gobarar ta yi ba, amma zan iya tabbatar muku da cewa duk bayanan da suka shafi harkokin kudi da hada-hadarsu, basu samu wata matsala ba,” Yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan wadannan gobara-gobaran dake faruwa duk da cewa ma’aikata sun kwashe fiye da makonni biyu basu zuwa aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *