FG ta gimtse shirin bayar da tallafin N20,000 a jihohi hudu

Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa ta gimtse shirin bayar da tallafin jin kai a jihohin Najeriya guda hudu. A cewar wani jawabi da ministar jin dadi da walwala, Sadiya Umar Farouq, ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa an janye shirin daga jihohin ne saboda saba ka’idojin yarjejeniyar bayar da tallafin da ‘yan kwangila suka yi a jihohin. “Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangila ga wasu cibiyoyi don su raba kudin tallafin jin kai a jihohin Bayelsa, Akwa Ibom, Abia da Zamafara. “An gimtse shirin a jihohin ne bisa biyayya ga tsarin bankin duniya domin tabbatar da cewa an fara biyan kudin tallafin ga jama’a a ranar 28 ga watan Afrilu ko kafin ranar,” a cewar jawabin da kakakin ministar, Salisu Dambatta, ya saka wa hannu. 

Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta amince da jinkiri ko karbar wani uzuri wajen biyan talakawa tallafin kudin jin kai N20,000 a jihohin hudu da sauran jihohin kasa ba. 

“Ba zamu lamunci gazawar cibiyoyin aika kudin ga talakawa ba. Gwamnatin tarayya ba za ta bari ‘yan kwangila su haddasa jinkiri wajen aika wa talakawa tallafin kudin ba,” kamar yadda ministar ta kara da cewa. 

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ma’aikatar jin dadi da walwalar jin dadi a kan ta cigaba da rabon kudi da kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadin matsin annobar covid-19. Kazalika, ya bayar da umarnin kara sunayen mutum miliyan daya a cikin rijistar talakawa miliyan 1.6 da ke cin moriyar shirin, duk domin a ragewa jama’a radadin matsin tattalin arziki da annobar coronavirus ta haifar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *