An sake sallaman mutane 8 da suka warke daga cutar Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta sake sallamar masu cutar Coronavirus takwas da suka samu waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaba ta jihar. Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne ta shafin Tuwitan gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu. Gwamnan yace: “Muna sake samun labarai masu dadi daga asibitin jinyar cututtukarmu dake Yaba.“ “An samu karin mutane takwas: mata biyu da maza shida da gwajinsu ya nuna cewa sun warke gaba daya daga cutar COVID19. Tuni an sallamesu kuma sun koma wajen iyalansu.“ “Hakan ya kawo adadin mara lafiya da mukayi jinya kuma muka sallama daga asibitocinmu zuwa 69.“ “Dan Alah mu cigaba da bin dukkan shawarin masana kiwon lafiya.“ A yanzu haka, jihar Legas ce jiha mafi yawan masu dauke da cutar inda mutane 192 cikin 343 na kasa gaba daya suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *