PDP ta kai INEC Kotu, ta bukaci a hana Tinubu da Peter Obi canza abokan takararsu a zaben 2023 mai zuwa.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da karar INEC a kotu, ta na neman tursasawa hukumar zaben ta hana APC da LP shiga zaben shugaban kasa.

Punch ta ce Lauyoyin PDP su na so Alkali ya hana ‘dan takaran APC, Bola Tinubu da na LP, Peter Obi damar canza abokan takararsu a zaben 2023 mai zuwa.

Jam’iyyar PDP ta kai kara ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja a tsakiyar makon nan. A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022, ana kalubalantar maye guraben Doyin Okupe da Kabir Masari da Kashim Shettima da Datti Baba-Ahmed.

Lauyoyin jam’iyyar hamayyar sun kuma roki Alkali ya haramtawa Tinubu da Obi takara a 2023 muddin ba su dawo da Masari da Dr. Okupe a tikitinsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *